ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto ministan kudi da kuma na ayyukan noma na kasar ta Zimbabwe suna fadar haka a jiya Litinin. A cikin watan da ya gabata ne gwamnatin kasar ta Zimbabwe ta amince ta biya dalar Amurka biliyon $3.5 ga fararen fata wadanda gwamnatin tsahon shugaban kasar kuma marigayi Robert Mugabe ta kwace gonakinsu.
Gwamnatin Mugabe ta aiwatar da wannan shirin don karfafa bakakin fatar kasar, wadanda akayiwa mulkin mallaka na lokaci mai tsawo. Labarin ya kara da cewa idan mayar da gonaki ga fararen fatan ba zai yu ba, to gwamnatin kasar za ta basu wasu gonakin a wasu wurare daban.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa mayarwa fararen fatar gonakinsu na da, yana da matukar wuya. Kafin haka dai shugaban kasar ta Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya bayyana cewa, maida mallakan gonaki ga fararen fata ya na da matukar wuya, don haka abun gwamnatin kasar za ta iya yi, shi ne biyan kudaden diyya ga fararen fatan ko danginsu.
Kungiyar fararen fata manoma a kasar Zimbabwe dai, ta bayyana cewa yawan manoma fararen fata a kasar ya ragu daga 4,500 zuwa 200 kacal a halin yanzu.
342/